IQNA

Kungiyar Jihadul Islami Ta Yi Kira Da A Kalubalanci Makircin Kulla Alaka Da Isra’ila

22:58 - September 05, 2020
Lambar Labari: 3485151
Tehran (IQNA) kungiyar jihadul Islami ta kirayi kasashen musulmi das u kalubalanci makircin da wasu suka bullo da shi na kulla hulda da yahudawan Isra’ila.

Tashar almasirah ta bayar da rahoton cewa, Ahmad Almudallil daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul Islami ya bayyana cewa, kungiyar jihadul Islami tana kira ga kasashen musulmi da su kalubalanci makircin da wasu gwamnatocin larabawa suka bullo da shi na kulla hulda da yahudawan Isra’ila.

Ya ce wannan babban abin kunya ne a daidai lokacin da Isra’ila take kashe  mulmi falastinawa, a lokacin ne kuam wasu sarakunan larabawa suke kulla hulda da ita domin kyautata mata, tare da mantawa da halin da ‘yan uwansu Falastinawa suke ciki.

Ya kara da cewa wajibi ne akn dukkanion muslmi su kalubalanci wannan makirci da maiiya musulmi da masu munafuntar musulmi daga cikinsu suka bullo da shi.

Jagoran na jihadul Islami ya ce idan yahudawa suka gama da Falastinu, to kuma Makka da Madina ba za su tsira ba, domin kuwa ga halin da birnin Quds yake cikia  halin aynzu kowa yana gani.

3921084

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Makka da Madina yahudawa
captcha