IQNA

‘Yan Majalisar Dokokin Burtaniya Sun Yi Allawadai Da Takura Wa Musulmi A China

22:49 - September 09, 2020
Lambar Labari: 3485167
Tehran (IQNA) Fiye da ‘yan majalisar kasar Burtaniya 100 ne suka yi tir da Allawadai da takurawa musulmin Igoir da gwamnagtin kasar China take yi.

Shafin yada labarai an City Am ya bayar da rahoton cewa, ‘yan majalisar dokokin kasar wadanda akasarinsu daga jam’iyyar Labour adawa suke, sun sanya hannu kan wata takarda, wadda suka yi kakkausar suka kan cin zarafin musulmi da gwamnatin China take yi.

‘Yan majalisar sun aike da wannan takada  zuwa ga jakadan kasar China a London Liu Ziaoming, domin ya isar da wannan sako ga gwamnatin kasarsa.

A cikin watan Yulin day a gabata, sakataren harkokin wajen Burtaniya ya zargi gwamnatin China ta takura wa musulmin Igoir, tare da killace fiye mutane miliyan daya daga cikinsu a wani wuri mai kama da gidan kaso.

3921848

 

captcha