A cikin makon da ya gabata ne wani ba Falasdine mai suna Dawood Alkhatib ya rasu a gidan yari na Isra'ila , saboda sakaci wajen bashi kula na likitoci da kiwon lafiya a lokacin da ya ke bukatar hakan.
Sai dai a cikin watan Yulin da ya gabata ne wata babbar kotu a Isra'ila ta yanke hukuncin cewa Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila ba sa da hakkin a kula da lafiyarsu har’ila yau ba su da hakkin yi masu tsare-tsaren hana yaduwar cutar korona a cikin gidajen yarin da ake tsare da su.
Kafin haka dai Falasdinawa sun koka kan cewa Isra'ila tana sakaci wajen kula da lafiyar Falasdinawan da take tsare da su a gidajen kaso, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu, wanda kuma yana daga cikin dalilan tafiyar wannan tawaga ta Masar zuwa Falastinu.
3922095