IQNA

Abdulsalam: Ya Kamata A Rusa Kungiyar Kasashen Larabawa Domin Ba Ta Da Amfani

23:48 - September 11, 2020
Lambar Labari: 3485172
Tehran (IQNA) Kakakin Kungiyar Ansarullah ta Yemen Muhammad Abdussalam ya ce ya kamata a rusa kungiyar kasasen larabawa, domin ba ta da wani amfani.

Kakakin kungiyar ta “Kungiyar Ansarullah” ta kasar Yemen, Muhammad Abdussalam’ ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Idan har Palasdinu za ta to wajen kungiyar ta nemi ta fitar da wani matsayi, sannan ta kiya, to wannan kungiyar ta mutu ya kamata a haka kabari a rufe ta.

Muhammad Abdussalam ya yi Allah wadai da babbar murya akan yadda kungiyar hadin kan kasashen larabawan ta ki yarda da bukatar Falasdinawa.

Kakakin na kungiyar Ansarulalh ya kuma ce; Al’ummun wannan yankin suna a raye, kuma kasashen da su ka yi tir da wannan matsayin na kungiyar hadin kan kasashen larabawa a cikin kungiyar su ne abin dogar0 da jingina wajen goyon bayan hakkin palasdinawa.

A tsakiyar mako mai karewa ne dai kungiyar ‘yanto Palasdinu ta PLO ta bakin sakatarenta, Sa’ib Uraiqat ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar Larabawan idan har ta amince da daftarin kudurin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar mata akan hulda da Isra’ila.

 

3922244

 

 

 

 

captcha