IQNA

Haniyya: Al'ummar Falastinu Ba Ta Yafe Wa Larabawa Masu Kulla Hulda Da Isra'ila Ba

23:03 - September 13, 2020
Lambar Labari: 3485181
Tehran IQNA, Hamas ta bayyana cewa makirci da ha’inci na sarakunan larabawa ba zai iya karya gwiwar al’ummar falastinu ba.

Kungiyar gwagwarmayar falastinawa ta Hamas ta bayyana cewa, makirci da ha’inci na sarakunan larabawa ba zai iya karya gwiwar al’ummar falastinu wajen neman hakkokinsu da yahudawan sahyuniya suka haramta musu ba.

Shugaban kungiyar ta Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ‘yan mamaya da sarakunan larabawa ke yi, na a matsayin cin amanar dukkanin al’ummar Falastinu da larabawa baki daya.

Ya ce kulla wannan alaka ba zai ta baiwa Isra’ila halasci ba, kamar yadda kuma hakan ba zai taba halasta zaluncinta akan al’ummar Falastinu da sayran al’ummomin musulmi da na larabawa ba.

Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Bahrain ta bi sahun kasar hadaddiyar daular larabawa wajen kulla alaka ta diflomasiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Al’ummomin larabawa a kasashe daban-daban suna ci gaba da bayyana mataki da cewa ha’inci ne, kuma ba da yawunsu ake yin hakan ba.

3922315

 

captcha