Jami’an ‘yan sanda na birnin Toronto a kasar Canada sun ce sun dukufa kan gudanar da bincike, domin gano wadanda suke da hannu a kisan wani musulmi da aka yi a cikin masallacin cibiyar musulmi ta International Muslim Organization of Toronto.
Cibiyar ta fitar da bayanin da ke cewa, tana kira ga dukkanin musulmi a birnin da ma kasar ta Canada da su kwantar da hankulansu bayan faruwar wanna lamari, kuma cibiyar tana ci gaba da bin kadun lamarin ta hanyoyin da suka dace.
An kashe mutumin ne a cikin masallaci bayan sallar isha’i, ta hanyar daba masa wuka a bangarori daban-daban a cikin jikinsa, inda a nan take ya rasu a cikin masallacin.
Jami’an ‘yan sada sun ce wasu shedun gani da ido sun tabbatar da cewa sun ga shiga wani mutum ramamme a cikin cikin masallaci sanye da bakaken kaya, daga bisani kuma ya fita daga cikin masallacin, inda bayan haka ne aka fahimci cewa an yi kisan kai a wannan masallaci.
3922569