IQNA

22:04 - September 14, 2020
Lambar Labari: 3485185
Tehran (IQNA) Jaridar yahudawan Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta bayyana cewa, kulla alaka tsakanin Bahrain da Isra’ila, zai amfanar da Trump da Bin Salman.

Kamfanin dillancin labaran MAA ya bayar da rahoton cewa, jaridar yahudawan ta ce, ko shakka babu kasar Bahrain ba wata kasa ce mai wani muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya ko yankin tekun Fasha ba, amma kulla wannan alaka zai kara tabbatar da halascin Isra’ila a matsayin kasa, wadda hatta kasashen larabawa sun amince da ita a hukumance.

Haka nan kuma jaridar ta ce tun fiye da shekaru ashirin da suka gabata akwai alaka mai karfi tsakanin wadannan kasashe da kuma Isra’ila, musamman hadaddiyar daular larabawa, amma fitowa fili a sanar da wannan alaka a hukuamnce babban lamari ne mai matukar muhimmanci ga Isra’ila.

Kamar yadda kuma ta yi ishara da cewa kasar Bahrain mafi yawan mutanen kasarta mabiya mazhabar shi’a ne, sabanin kasashen Oman da hadaddiyar daular larabawa.

Bugu da kari kan haka kuma ta ce wannan lamari ya faru ne bayan cimma matsaya tsakanin Trump da kuma Muhammad Ben Salman yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya, wanda hakan zai kara daga matsayin Ben Salman a matsayin mai karfin fada a ji a yankin, kamar yadda shi kuma Trump hakan zai taimaka masa a yakin neman zabe.

3922640

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: