IQNA

An Bude Cibiyoyin Karatu Da Hardar Kur'ani 69 A Masar

23:36 - September 17, 2020
Lambar Labari: 3485195
Tehran (IQNA) ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da bude cibiyoyin koyar da hardar kur'ani mai sarki guda 69 a kasar.

Shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Mukhtar Juma'a ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya sanar da cewa, sun bude cibiyoyin koyar da hardar kur'ani mai sarki guda 69 a kasar ta Masar.

Ya ci gaba da cewa wadannan cibiyoyi an bude su a wasu manyan masallatai na wasu biranan kasar, inda malamai da limaman masallatan ne za su jagoranci shirin.

Ya ce babbar manufar hakan ita ce kara yada sh'anin kur'ani ta hanyoyin da suka dace, tare da kokarin ganin cewa an kakkabe hannun masu tsattsauran ra'ayi, wadanda suke yin amfani da hakan wajen sakawa yara akidu marassa kyau da sunan kur'ani, har ya kai su ga shiga ayyukan ta'addanci.

 

3923536

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha