IQNA

23:38 - September 21, 2020
Lambar Labari: 3485206
Tehran (IQNA) yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna sun kutsa kai a cikin masallacin Aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Falastine ya bayar da rahoton cewa, yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna sun kutsa kai a cikin masallacin Aqsa mai alfarma tare da keta alfarmar wannan masallaci.

Rahoton ya ce tun kafin zuwan yahudawa jami’an ‘yan sandan Isra’ila sun isa wurin dauke da makamai, inda suka ba su kariya domin tabbatar da cewa musulmi ba su hana yahudawan shiga cikin masallacin mai afarma ba.

Kwamitin da ke kula da harkokin masallacin Quds ya sanar da cewa, wannan mataki na tsokana da yahudawan suke dauka a kowane lokaci da nufin bakantawa musulmi.

Bayanin kwamitin ya ce a daidai irin wannan lokacin ne kuma abin takaici, wasu daga cikin shugannin larabawa suke ta hankoron ganin sun mika kai ga Isra’ila da neman kullaka alaka da ita.

 

3924450

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: