IQNA

Gwanatin Falastinu Ta Ti Watsi Da Shugabancin Kungiyar Kasashen Larabawa

22:32 - September 23, 2020
Lambar Labari: 3485211
Falastinu ta sanar da cewa, ta ajiye jagorancin kungiyar kasashen larabawa da take yi, sakamakon yadda kungiyar ta goyi bayan kulla alaka da Isr’ila.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Falastinu ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin jin dadinta, kan yadda kungiyar kasashen larabawan taki amincewa da daftarin kudirin da ta gabatar, na neman kungiyar ta yi Allawadai da duk wani nau’in kulla kawance da Isra’ila a tsakanin kasashen larabawa.

Ministan harkokin wajen Falastinu Riyad Maliki ya bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne domin tabbatar wa duniya cewa ba za su taba yarda a sayar da Falastinu ga yahudawan Isra’ila ba.

Ya ce: abin takaici ne yadda wasu daga cikin kasashen larabawa ne a halin yanzu suka dauki nauyin yin tallar siyasar Isra’ila a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi, tare da mantawa da batun Falstinu da kuma halin da Isra’ila ta jefa Falastinawa.

A haka ministan harkokin wajen Falastinu ya ce sun ajiye shugabancin karba-karba na kungiyar kasashen larabawa, wanda a halin yanzu yake a hannun gwamnatin Falastinu.

3924648

 

 

captcha