IQNA

22:28 - September 24, 2020
Lambar Labari: 3485215
Tehran (IQNA) cibiyar da ke kula da lamurran fursunonin Falastinawa a gijane kason Isra'ila ta sanar cewa fursunonin za su fara yajin cin abinci.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, sakamakon yadda Isra'ila take gallaza wa falastinawa da take tsare da su a cikin gidajen kaso saboda dalilai na siyasa, fursunonin za su fara yajin cin abinci a gidajen kaso biyar na Isra'ila.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan Isra'ila take ta kara tsananta daukar matakai na takura ma falastinawa ne, inda wasu suna rasa rayukansu sakamakon rashin kula.

baya ga haka kuma tana ci gaba da kame wasu falastinawan musamman masu nuna adawa da shirin yahudawa na mamaye wasu yankunan falastinawa.

 

3925174

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: