IQNA

Jami’an Tsaron Najeriya 15 Sun Rasa Rayukansu A Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Gwamna Zulum

22:58 - September 26, 2020
Lambar Labari: 3485218
Tehran (IQNA) mutane 15 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno a jiya Juma’a.

Majiyoyin tsaro daga Najeriya, na cewa, mutane 15 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno a jiya Juma’a a kusa da garin Baga dake kusa da tafkin Chadi.

Mutanen dai mambobi ne na tawagar gwamnan jihar Bornon, Babagana Umara Zulum, wanda ya kubuta daga harin, wanda ake dangantawa dana mayaka reshen kungiyar ‘yan ta’addan takfir dake a arewa maso gabashin kasar.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaran AFP, cewa daga cikin wadanda harin ya rutsa da su da akwai ‘yan sanda takwas, da sojoji uku da kuma wasu mambobi hudu na ‘yan kato da gora

Bayanai sun ce mayakan sun yi amfani da makamai masu sarrafa kansu da gurneti gurneti a daidai lokacin da tawagar gwamna Zulum ke wucewa a cikin wani kauye dake kusa da hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kaiwa tawagar Gwaman na jihar Borno hari a baya baya nan.

 

3925456

 

 

 

 

 

captcha