IQNA

An Kirayi Majalisar Dinkin Duniya Da Ta Yi Adalci A Shiga Tsakanini Kan Rikicin Yemen

19:46 - September 28, 2020
Lambar Labari: 3485226
Tehran (IQNA) Shugaban majalisar koli ta juyi a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya bayyana cewa aikin majalisar dinkin duniya a Yemen shi ne shiga tsakani.

Alhuthi ya bayyana haka ne a jiya a zantawarsa da manema labarai a birnin San’a, inda ya kara jaddada cewa akowane lokaci a shirye suke domin warware matsalar da aka jefa kasar yemen a cikinta.

Ya ce tuni sun gabatar da shawarwari kan abubuwan ad suke ganin su ne asasi na kawo karshen halin da aka jefa kasar Yemen a ciki, inda suka mika wa majalisar dinkin duniya wadannan shawarwari da kuma mahangar da suke da ita.

Daga ciki abubuwan da suka jaddada wa kansu har da kawo karshen kisan kiyashi da masarautar Al Saud da ‘yan korenta suke yi kan al’ummar kasar, tare da bayar da dama ga al’ummar kasar su warware matsalolinsu da kansu ta hanyar tattaunawa da junansu.

Baya ga haka kuma sun bukaci majalisar majalisar dinkin duniya da ta zama mai shiga tsakanin domin ganin an cimma maslaha kan rikicin na yemen, amma abin takaici sau da yawa tana nuna karkata ga masu kisan mata da kananan yara a kasar.

3925549

 

 

 

 

captcha