Firayi ministan kasar Morocco Sa’aduddinin Al’usmani ya sanar da cewa, matukar dai ba a kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta ba, to kulla duk wani sulhu da Isra’ila ba shi da wani amfani.
Firayi ministan na kasar Morocco ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a jiya a gaban babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara.
Ya ce yi wa al’ummar Falastinu adalci tare da warware matsalolinsu da kuma mayar musu da hakkokinsu da aka kwace musu, shi ne kadai hanyar zaman lafiya yankin gabas ta tsakiya.
Haka nan kuma ya kara da cewa, Isra’ila ummul haba’isin duk wasu matsaloli da suke faruwa, kuma dole ne ta yi aiki da dokokin kasa da kasa, tare da dakatar da ginin matsugunnan yahudawa da take yia cikin yankunan Falastinawa, kuam ta janye daga yankunan da ta mamaye.
3925626