Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa a yau Juma’a jami’an sojin Isra’ila sun yi dirar mikiya a gidan Sheikh Hassan Yusuf daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas, kuma suka kame shi.
Rahoton sun tafi shi wani wuri da ba a sani ba, duk kuwa da cewa a cikin watan Yulin da ya gabata ne ya fito daga kurkukun Isra’ila, bayan ya shafe watanni 15 a tsare.
Kimanin shekaru 23 a rayuwar Sheikh Hassan Yusuf ya yi su ne a cikin gidajen kurkuku daban-daban na yahudawan Isra’ila.
A halin yanzu dai yana fama da matsaloli daban-daban na rashin lafiya da ke bukatar kulawa ta musamman.
3926733