IQNA

Gwamnatin Isra’ila Na Shirin Gina Matsunnan Yahudawa 4500 A Cikin Yankunan Falastinawa

22:50 - October 05, 2020
1
Lambar Labari: 3485249
Tehran (IQNA) gwamnatin yahudawan Isra’ila shirin gina matsugunnan yahudawa kimanin 4500 a cikin yankunan Falastinawa.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin yahudawan Isra’ila shirin gina matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna guda  4500 a cikin yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

A gobe ne firayi ministan Isra’ila zai gabatar da wannan kudiria  zaman majalisar ministoci, domin amincewa da kudirin.

Kafin wanna lokacin dai Benjamin Netayahu ya bayyana cewa, sakamakon kulla alaka da kasashen larabawa za a jinkirta aiwatar da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yamamcin kogin Jordan.

A cikin bayaninsa na baya-bayan nan, ya bayyana cewa tun da sun cimma matsaya tare da wasu kasashen larabawa, kuma babu batun dakatar da mamaye yankunan Falastinawa a cikin yarjejeniyar da suka cimmawa da kasashen hadaddyar daular larabawa da Bahrain, saboda haka babu wani dalili da zai sanya Isra’ila ta yi jinkiri wajen ci gaba da aiwatar da shirinta.

3927247

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Zakariyya abubakar danbaba
0
2
Hakan cinzarafin Dan adamne baikamata isra'ila asameta aiwatardahakanba
captcha