IQNA

Sudan: Kungiyar Ikhwan Ta Ce Kulla Hulda Da Isra’ila Cin Amanar Falastinawa Ne

23:13 - October 10, 2020
Lambar Labari: 3485262
Tehran (IQNA) Kungiyar Ikhwanul Muslimin a kasar Sudan ta bayyana kulla hulda tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila a matsayin cin amana ga al’ummar Falastinu.

Shafin arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, jagoran kungiyar Ikhwan a kasar Sudan Adel Ali ya bayyana cewa, masu tunanin cewa kulla alaka tsakanin Sudan da Isra’ila zai kawo karshen matsalolin da kasar take ciki, suna tafka baban kure, domin kuwa yin hakan babu abin da zai kara jawowa kasar sai matsaloli.

Ya ce shin dukkanin kasashen da suke da alaka da ba su fama da matsaloli na tattalin arziki ne? akwai da dama daga cikinsu suna cikin matsaloli, kuma kasashen larabawan da suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ba al’umma ne ke mulki a  kasashnsu ba, mulki ne na mulukiyya, wanda iyalan gida guda ne suke mamaye komai na al’ummar kasa.

Ya ce abin da Sudan take bukata  ahalin yanzu shi ne tsari na gudanarwa, wanda zai ba ta daar samar da tsare-tsare da za su inganta tattalin arzikinta, da kuma bude huldodi tare da sauran kasashen duniya.

Haka nan nan ya kara jaddada matsayin kungiyarsu na cewa, matukar Isra’ila tana ci gaba da mamaye kasar Falastinu tare da hana Falastinawa hakkokinsu, ba za su taba amincewa da ita a matsayin halastacciyar kasa ba.

3928184

 

 

captcha