Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana tabbatar da tsaro a cikin kowace al’umma, a matsayin babban gishikin tabbatuwar sauran bangarori na jin dadin rayuwar al’umma.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau a lokacin da yake tarbar daliban jami’oin koyar da ayyukan soji na kasar, wanda aka gudanar ta hanyar hotunan yanar gizo.
Jagoran ya bayyana cewa, aikin tabbatar da taro a cikin al’umma shi ne babban gishi na na tabbatuwar sauran bangarori, domin kuwa duk al’ummar da ta rasa tsaro, to kuwa tarasa sauran bangarorin masu muhimmanci a cikin al’umma, kamar harkar ilimi da shari’a da sauransu, domin kuwa ba ta cikin natsuwa.
Ya ce mun ga yadda jami’an tsaro suke bayar da gusunmawa a bangarorin ci gaban rayuwar al’umma, da hakan ya hada da gina madatsun ruwa, hanyoyi, bangaren kiwon lafiya, kamar yadda muka ga jami’an tsaro sun bayar da gagarumar gudunmawa a bangaren ayyukan yaki da cutar corona, wanda hakan babban abin alfahari ga kasa.
3928754