IQNA

Fiye Da Kashi Casa’in Da Biyar Na Larabawa Ba Su Goyon bayan Kulla Alaka Da Isra’ila

22:53 - October 18, 2020
Lambar Labari: 3485287
yahudawa masu bincike sun gano cewa kashi casa’in da biyar cikin dari na larabawa basu goyon bayan kulla alaka da Isra’ila.

Jaridar Mana Post ta kasar Bahrain ta bayar da rahoton cewa, Wasu fitattun masana yahudawa masu bincike a Isr’ila sun bayar da rahoton cewa, fiye da kashi casa’in da biyar cikin dari na larabawa a kasashen Bahrain da Emerate ba su goyon bayan kulla alaka da Isra’ila da kasashensu.

Rahoton da yahudawan suka fitar wanda wasu daga cikin kafofin yada labaran Isra’ila suka watsa ya nuna cewa, sarakunan larabawa masu son samun kusanci da gwamnatin Amurka da suke yi mata biyayya sau da kafa ne suke son kulla alaka da Isra’ila.

Bayanin yace, bisa ga binciken da aka gudanar a kasashen larabawa, musammaa  kasashen Bahrain da UAE da suka kulla alaka da Isra’ila, an iya gano cewa fiye da kashi casa’in da biyar cikin dari na larabawan basu goyon bayan wannan kulla alaka, maimakon haka ma suna adawa da shirin.

Bisa ga abin da wanann rahoton ya bayyana cewa, Iran da kuma kungiyoyin Hizbullah da Hamas su ne suka jawo bakanta Isra’ila a cikin zukatan larabawa.

3929783

 

 

captcha