IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai da Kai Wa Musulmi Mata Hari A Kasar Faransa

22:43 - October 22, 2020
Lambar Labari: 3485298
Tehran (IQMNA) cibiyar Azhar a kasar Masar ta yi Allawadai da harin da aka kaiwa wasu mata musulmi biyu da suke sanye da lullubi a Faransa.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya babyar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar, babbar cibiyar addini ta Azhar ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da aka kaiwa wasu mata musulmi biyu da suke sanye da lullubi a Faransa a ranar Lahadi da ta gabata.

Bayanin ya ce babu wani dalili da zai sanya a kaiwa wani hari kawai saboda addininsa, wannan ya sabawa ‘yan adamtaka, kuma ya zama wajibi a dauki matakan tunkarar irin wannan tsatsauran raayi na nuna kyama da musulunci wanda shi ne yake haifar da wasu matsalolin.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da nuna halin ko in kula da keta alfarmar abubuwa masu tsarki na addinin muslunci da hukumomin kasashen turai suke yi, tare da bayya hakana  matsayin wani bangare da ke kara jawo irin wadannan matsaloli.

A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu masu tsananin kin jinin musulmi a kasar Faransa suka kaddamar da hari kan wasu mata msuulmi biyu ‘yan asalin kasar Aljeriya, a lokacin da suke tafiya sanye da lullubi a kansu.

 

3930783

 

 

 

captcha