IQNA

Masu Kulla Alaka Da Isra’ila Sun Yi Gum Da Bakunansu Kan Cin Zarafin Ma’aiki

23:00 - October 27, 2020
Lambar Labari: 3485311
Tehran (IQNA) al’ummomin musulmi da na larabawa na ci gaba da mayar da martani a kan gwamnatocin larabawa da suka kulla hulda da Isra’ila kan yadda suka yi gum da bakunansu dangane da cin zarafin ma’aiki (SAW).

A daidai lokacin masu tsananin kiyayya da addinin muslunci suke ci gaba da yin shishigi a kan addinin muslunci da hakan har ya kai ga tozarta matsayin ma’aiki (SAW) gwamnatocin kasashen larabawa da suka kulla alaka da Isra’ila da masu hankoron kulla wannan alaka sun yi shiru da bakunansu.

Wannan mataki da nuna halin ko in kula da mafi yawan gwamnatocin larabawa suka nuna kan cin zarafin manzon Allah (SAW) musamman masu hankoron kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, hakan ya bakanta rayukan mafi yawan al’ummomin kasashen larabawa.

Da dama daga cikin al’ummomin kasashen larabawa na ci gaba da aikewa da sakoni a shafukan sada zumunta na yanar gizo, inda suke yin Allawadai da sarakuna da shugabaninsu, kan yadda suka nuna rashin damuwarsu da keta alfarmar manzo da kuma addinin muslunci da ake yi a kasar Faransa.

3931487

 

captcha