IQNA

22:50 - November 01, 2020
Lambar Labari: 3485327
Tehran (IQNA) shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana nadamarsa da goyon bayan da ya bawa kamfanin jaridar Chali Ebdo wacce ta buga zane na wulakanta manzon All..(s).

Shafin yada labarai na vetogate.com ya bayar ad rahoton cewa, shugaban Macron yana fadar haka ne a shafinsa na Twitter inda yake cewa, a kasar Faransa dukkan mabiya adddinai daban-daban suna gudanar da ayyukan ibadansu ba tare da tsongoma ba, sannan shi a karan kansa baya adawa da wani addini.

Har’ila yau shugaban yayi hira da tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar inda ya kara nana cewa ya fahinci irin yadda musulmi a duniya suke ji bayan buda zane-zanen wulakanta manzon All…wanda jaridar Charlie Hebdo ta yi. Goyon bayan da ya bawo jaridar ba yana nufin batawa musulmi rai ba.

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne shugaban ya bayyana goyon bayansa ga abin da Jaridar ta yi, na batanci, sannan yana ganin yin hakan yana daga cikin ‘yancin fadin albarkacin bakin da yan kasar Faransa suke da shi.

3932526

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: