IQNA

Shugaba Rauhani na Iran:
22:50 - November 04, 2020
Lambar Labari: 3485334
Tehran (IQNA) Shugaba Rauhani ya ce canja siyasar Amurka shi ne ba zaben shugaban kasa ba.

Shugaban kasar Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, zaben wani mutum a matsayin shugaban kasa a Amurka ba shi ne ke da muhimmanci a wurin Iran ba, abin da ke da muhimmanci shi ne sauya salon siyasar Amurka.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yau Laraba, a lokaci da yake gabatar da wani jawabi a zaman majalisar ministocin kasar a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa; ko kadan Iran ba ta damu da sakamakon zaben shugaban kasar Amurka ba, domin kuwa matukar ba a samu canji a salon siyasar Amurka ba, babu wani banbanci tsakanin dukkanin ‘yan takarar da za su kafa gwamnati.

Rauhani ya ci gaba da cewa, idan Amurka ta ajiye halayyarta ta yin hawan kawara  akan dokokin kasa da kasa, tare da yin aiki da yarjejeniyoyon kasa da kasa da ta rattaba hannu a kansu, da kuma dawowa a cikin yarjejeniyar nukiliya da aka kulla tae da Iran, a lokacin za ta ga canji daga Iran.

A jiya ma jagoran juyin juya hali na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yayin da yake gabatar da jawabi kan maulidin manzon Allah ya yi ishara da wannan matsaya ta kasar Iran, inda ya jaddada cewa matsin lambar Amurka da kakaba takunkumi ba zai iya sanya Iran ta mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba.

Akwai sabanin mahanaga tsakanin Trump da Joe Biden kan yadda ya kamata su tafiyar da siyasar Amurka dangane da kasar Iran, inda Biden ke ganin yin amfani da hanyoyi na siyasa zai dacewa, yayin da Trump ya fifita yin amfani da barazana da kakaba takunkumi, domin tilasta Iran ta mika wuya ga manufofin Amurka.

 

3933201

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: