IQNA

23:44 - November 06, 2020
Lambar Labari: 3485340
Tehran (IQNA) hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake bullar wata annoba a duniya.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da hukumar lafiya ta duniya ta fitar, yi gargadi ga kasashen duniya kan cewa akwai yiwuwar wata sabuwar annoba ta sake bulla.

Bayanin ya ce daya daga cikin muhimman abubuwan da zaman taron ranakun 9 zuwa 14 na jami’an hukumar zai mayar da hankalia  kansu shi ne batun yadda ya kamata kasashen duniya su zama cikin shiri domin fuskantar abin da ka iya faruwa.

Hukumar ta ce a lokacin da cutar corona ta bulla da kuma lokacin da ta fara yin kamari, kasashen duniya da dama sun yi namijin kokari wajen tunkararta, wanda hakan yasa duk da illar da cutar ta yi, amma kokarin da aka yi ya dakushe kaifinta.

Daftarin kudirin hukumar ya kirayi dukkanin hukumomi na duniya da su kara zage dantse, domin annobar da ake hasashen cewa za ta iya sake bulla a nan gaba, za ta zama mai muni matuka.

 

3933530

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hukumar lafiya ta duniya ، annoba ، duniya ، gargadi ، hasashen cewa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: