IQNA

23:32 - November 08, 2020
Lambar Labari: 3485347
Tehran (IQNA) shugaban cibiyar Azhar ya bayyana cewa dole ne a dauki matakan kawo karshen tsatsauran ra’ayi a duniya.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babban malamin cibiyar Azhar a kasar Masar Ahamd Tayyib ya bayyana cewa, lokaci ya yi da al’ummomin duniya za su hada karfi domin kawo karshen duk wani na’uin ta’addanci da sunan addini.

Ahmad Tayyib ya bayyana cewa ya kadu matuka bayan samun labarin kai harin birnin Vienna na kasar Austria, inda ya bayyana cewa hakika yana taya dukaknin wadanda lamarin ya shafa alhini, tare da yin Allawadai da wannan aiki na ta’addanci.

Ya ci gaba da cewa, duk wani aiki na ta’addanci da wani zai akata da sunan addinin muslucni, to dole ne kowa ya sani cewa ba da sunan musulunci ya aikata haka ba, kuam bay a wakiltar muslucni ko kuma koyarwa ta hanyar aikata hakan.

Malamin ya kara da cewa, irin wanan aiki na ta’addanci da tsatsauran ra’ayi abin Allawadai ne daga kowane mutum ya aikata hakan da suna kowane irin addini ne, kuma addinai da aka saukar daga sama babu wani daga cikinsu da ke kira zuwa ga irin wannan aiki.

 

3933149

 

Abubuwan Da Ya Shafa: addinai ، ta’addanci ، Allawadai ، kasar Austria ، cibiyar Azhar ، kasar Masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: