IQNA

23:46 - November 11, 2020
Lambar Labari: 3485355
Tehran (IQNA) Iran tana jira ta ga kamun ludayin gwamnatin Amurka mai zuwa kafin yin hukunci a kan ayyukanta

Kakakin gwamnatin kasar Iran Ali Rabie ya bayyana cewa, Iran tana jira ta ga kamun ludayin gwamnatin Amurka mai zuwa kafin yin hukunci a kan ayyukanta.

A lokacin dav yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, kakakin gwamnatin kasar Iran Ali Rabie ya bayyana cewa, siyasar kasar Iran dangane ad kasar Amurka a bayyane take ga kowa a duniya, saboda haka babu wani canji dangane da haka, matukar ba an samu canji a cikin siyasar Amurka ba.

Ya ci gaba da cewa, kasar ta Iran tana la’akari da salon siyasa, ba mutane masu mulki a kasar Amurka, domin kuwa salon siyasar kasar dangane da kasashen duniya na neman yin mulkin mallaka da mayar da sauran kasashen duniya ‘yan amashin shata, shi ne abin da Iran ba ta yarda da shi ba, kuma ba za ta mika kai ga hakan ba.

Dangane da zabukan da aka gudanar a kasar ta Amurka kuwa, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati mai zuwa ta dauki darasi daga irin tabargazar da gwamnati da wa’adin ke karewa ta yi ta tafkawa, wanda hakan ya kara zubar da kimar Amurka a duniya.

3934414

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: