IQNA

14:46 - November 12, 2020
Lambar Labari: 3485359
Tehran (IQNA) ana gudanar da shirin makon kusanto da fahimta  a tsakanin addinai a kasar Burtaniya.

Shafin yada labarai na MCB ya bayar da rahoton cewa, a cikin wanann makon ne ake gudanar da shirin kusanto da fahimtar juna a tsakanin addinai, domin kara samun lafiya da girmama juna tsakanin dukkanin mabiya addinai a kasar.

A daidai lokacin da gudanar da wannan shiri,a  daya bangaren kuma an samar da wani shirin hadin gwiwa tsakanin majami’oin mabiya addinin kirista da masallatan musulmia  kasar ta Burtaniya.

Wanann shirin hadin gwiwa tsakanin majami’oi da masallatai ana gudanar da shi ne a karon farko a kasar ta Burtaniya, inda masallatai da majami’oin mabiya addinin kimanin 20 suka shiga cikin shirin, inda kuma malaman kiristoci da malaman mulmi gami da limamai suke tattaunawa kai tsaye a tsakaninsu ta hanyar hotuann bidiyo.

Babban abin da suke yin dubi a kansa dai shi ne yadda za a kara karfafa dangantaka da fahimta tsakanin musulmi da kuma mabiya addinin kirista, da girmama fahimta da mahangar juna.

Wannan mataki na zuwa biyo bayan abubuwan da suka faru a kasar Faransa a cikin lokutan baya-bayan nan, wanda ya yi sanadiyyar kai hare-hare a kan masallatai da kuma wuraren ibada na mabiya addinin kirista, wanda dukkanin malaman musulmi da na kisrista ba su ji dadin faruwar hakan ba.

 

3934385

 

  

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: