IQNA

22:55 - November 15, 2020
Lambar Labari: 3485369
Tsohon ministan al’adu na kasar Senegal ya mayar da lambar yabo da gwamnatin kasar Faransa ta ba shi, biyo bayan cin zarafin manzon Allah da aka yi a kasar ta Faransa tare da izin gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na arabi 21 cewa, a cikin wani sako da ya wallafa wanda kafofin sadarwa na yanar gizo suka watsa, tsohon ministan al’adu na kasar Senegal Amadu Tijjani Woun ya bayyana cewa, ya mayar da lambar yabo ta bangirma ta kasar Faransa, wadda gwamnatin kasar Faransa ta ba shi domin girmama shi.

Ya ce ya rubuta ma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da wata wasika, wadda a ciki ya sheda masa cewa, ya dauki wannan matakin ne sakamakon yadda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayar da irin wannan lambar yabo ta kasar Faransa, ga malamin makarantar nan day a ci zarafin manzon Allah (SAW) ta hanyar nuna zanen batunci ga dailabnsa da kuma yin izgilia  kan manzon Allah.

Tsohon ministan ya ce Macron yana kokarin daga wani kaskantancen mutum ta hanyar ba shi lambar yabo da bangirma ta gwamnatin kasar Faransa, a kan haka ya mayar da irin wannan lambar yabo da Faransa ta shi  ga ofishin jakandancinta da ke birnin Dakar.

Al’ummomin musulmi a duniya dai sun nuna fushinsu matuka dangane yadda gwamnatin faransa ta fito a fili tana kare cin zarafin manzon Allah (SAW) a hukumance a kasar.

3935339

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tsohon ministan ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: