IQNA

22:57 - November 15, 2020
Lambar Labari: 3485370
Rahotanni daga kasar Sudan na cewa a yau Lahadi wata tawagar yahudawan Isra’ila ta isa birnin Khartum a yau.

Kamfanin dillancin labaran Rabubah News na kasar Sudan ya bayar da rahoton cewa, a yau wata tawagar yahudawan sahyuniya daga Isra’ila ta iso kasar Sudan, domin ci gaba da kara karfafa alaka tsakanin Sudan da Isra’ila.

A ranar Talata da ta gabata wata kungiyar yahudawan sahyuniya mai suna makan ta bayar da bayanin cewa,a ranar Lahadi mai zuwa wata tawagar yahudawa daga Isra’ila za ta nufi Sudan, domin ganawa da sabbin mahukuntan kasar.

Wannan dai ita ce tawagar yahudawan Isra’ila da ta isa kasar Sudan, tun bayan da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan din ta mika wuya bori yah au, inda ta amince da kulla hulda da gwamnatin yahudawan Isra’ila, domin Amurka ta cir eta daga cikin jerin kasashen da take kira masu daukar nauyin ta’addanci.

Majiyoyin sun ce tawagar yahudawan ta kunshi ma’aikata da kuma kwararru a bangarori daban-daban na ayyuka, amma babu jami’ai na siyasa a cikin tawagar.

Sudan ta amince ta kulla hulda da Isra’ila ne sakamakon matsin lambar da ta fukanta daga gwamnatin Trump na Amurka, da kuma yariman Saudiyya ami jiran gado Muhammad Bin Salman, da kuma yarima mai jiran gado na hadaddiyar daular larabawa.

 

3935296

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: