IQNA

22:50 - November 16, 2020
Lambar Labari: 3485372
Tehran (IQNA) Kungiyar tarayyar turai ta caccaki Isra’ila dangane da ci gaba da yin gine-gine a cikin yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

A cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Falastinu ya bayar, ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell ya bayyana cewa, ci gaba da yin gine-gine a cikin yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan, ya yi hannun rida da dukkanin dokoki da ka’idoji na kasa da kasa.

Ya ce abin da Isra’ila ke yi na ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa tare da gina matsugunnan yahudawa acikinsu abu ne mai matukar tayar da hankali, kuma tarayyar turai ba za ta taba amincewa da halascin hakan ba.

Kafin wannan lokacin mai magana da yawun kungiyar tarayyar Peter Stano ya bayyana cewa, matsayin kungiyar tarayyar turai dangane da gine-ginen Isra’ila na nan babu canji, kuma tarayyar za ta iya daukar dukkanin matakin da ta ga ya dace kan Isra’ila dangane da hakan.

A cikin watannin da suka gabata tarayyar turai ta yi barazanar kakaba wa Isra’ila takunkuman karya tattalin arziki, matukar ta aiwatar da shirinta na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan, inda daga bisani firayi ministan gwamnatin yahudawan ya sanar da dakatar da wannan shiri.

3935444

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: