IQNA

22:52 - November 17, 2020
Lambar Labari: 3485375
Tehran (IQNA) Kungiyar Nujaba A Iraki Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Kan duk Wani Shishigi Na Trump.

Kungiyar Gwagwarmaya Ta Nujaba A Kasar Iraki Ta Ce, Ita Da Kawayenta Suna Cikin Ko-Ta-Kwana Domin Mayar Da Martani Akan Duk Wani Gigi Na Shugaban Kasar Amurka Trump.

Babban magatakardar kungiyar ta Nujabah ta kasar Iraki, al-Ka’abi ya gargadi shugaban kasar Amurka akan duk wani gigi da zai yi, domin kawancen gwagwarmaya zai mayar da martani.

Shi da babban sakataren kungiyar ta gwgawarmaya ta kasar Iraki yana mayar da martani ne akan wasu rahotanni da suke magan akan cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana da shirin kai wasu hare-hare a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya, yana mai karawa da cewa; Kwancen gwagwarmaya yana cikin shiri domin mayarwa Trump mai tabin hankali da martani.

 

3935677

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Kwancen gwagwarmaya ، hare-hare ، gabas ta tsakiya ، shishigi ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: