IQNA

22:59 - November 18, 2020
Lambar Labari: 3485378
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Turkiya ta sanar da cewa, tana kokarin ganin an dawo da mutumin nan dan kasarta wanda ya tozarta kur’ani.

Shafin yada labarai na turkey-breaking ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Turkiya ta sanar da cewa, tana kokarin ganin an dawo da mutumin nan dan kasarta wanda ya tozarta kur’ani wanda ya gudu zuwa Rasha.

Baynain ya ce mutumin mai suna Ibrahim Atabi ya gudu zuwa kasar rasha ne bayan daya aikata wasu laifuka da ake nemansa domin hukunta shi a cikin kasar ta Turkiya.

Bayan isarsa kasar kuma ya rika aikewa da wasu hotunan bidiyo da yake dauka yana watsawa a shafukan sada zumunta, inda yake yin izgili da kur’ani da kuma yin kalamai na batunci dangane da kur’ani mai tsarki.

Wannan lamari dai ya bakanta ran mutanen kasar Turkiya, inda jama’a suke ta yin matsin lamba kan gwamnati da ta dawo da shi domin hukunta shi.

Gwamnatin Turkiya ta ce tana yin iyakacin kokarinta tare da tattaunawa da bangaren mahukuntan Rasha domin dawo da shi, domin kuwa bangaren shari’a na Turkiya na nemansa kan aikta wasu manyan laifuka 11 kafin ya tsere.

3935962

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: