IQNA

14:22 - November 22, 2020
Lambar Labari: 3485388
Tehran (IQNA) an nuna wani fallen shafin kur’ani mai tsarki mafi jimawa a duniya a kasar Burtaniya.

Shafin fansar da kayan tarihi na Christies ya bayar da bayanin cewa, an samu wani kur’ani wanda ake danganta shi da farkon bayyanar muslunci a lokacin manzon Allah, ko kuma zuwa lokacin Halifa Usman Bin Affan.

Francis Cyors daya daga cikin masana na addinin kirista a darikar katolika, kuma mai yin bayani kan ababen tarihi a dakin fansar da kayan tarihi na Christies ya bayyana cewa, wannan bangare na kur’ani yana komawa zuwa ga lokacin bayyanar muslunci, mai yiwuwa daya daga cikin musulmi ne a lokacin rayuwar manzon Allah ya rubuta shi.

A shekarar da ta gabata an yi wannan shafi kudi tsakanin fan dubu 250 zuwa fan 300, amma a bana an fansar da shi a kan kudi fan miliyan 1 da dubu 300.

Wani abun ban al’ajabi shi ne yadda wannan shafi da aka rubuta  akan fatar akuya ya wanzu tare da rubutunsa har zuwa wannan lokaci ba tare da ya baci ba, inda aka samu rubutun ayoyi na 82-98 a cikin surat maryam.

A kasar Burtaniya dai akwai kayan tarihi an al’ummomi daban-daba da suke ajiye a dakunan adana kayan tarihi, wanda wasu daga cikin mallakin wasu mutane ne da suka saye su da jimawa, wasu kuma  alokacin mulkin mallaka a kasashen msuulmi ne turawa suka sace su.

 

قدیمی‌ترین صفحات قرآن، زینت‌بخش مجموعه‌های هنر اسلامی در جهان
 
قدیمی‌ترین صفحات قرآن، زینت‌بخش مجموعه‌های هنر اسلامی در جهان
 
قدیمی‌ترین صفحات قرآن، زینت‌بخش مجموعه‌های هنر اسلامی در جهان

 

3936551

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: