IQNA

22:52 - November 22, 2020
Lambar Labari: 3485389
Tehran (IQNA) Shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murnar zagayowar ranar da Lebanon ta samu ‘yancin kai.

Shugaba Hassan Rauhani na kasar Iran ya aike wa takwaransa na kasar Lebanon da sakon taya murnar zagayowar ranar da kasar ta Lebanon ta samu ‘yancin kai daga 'yan mulkin mallaka.

A cikin sakon nasa shugaba Rauhani ya bayyana cewa:

Yana taya takwaransa shugaba Micheil Aoun da sauran dukkanin al’ummar kasar Lebanon zagayowar ranar da kasar ta samu ‘yancin kai daga turawa ‘yan mulkin mallaka.

Ya ce a cikin shekarar da ta gabata kasar Lebanon ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa, amma sakamakon hikimar jagororin al’ummar kasar, a  karkashin shugabancin Aoun, kasar ba ta fada cikin mawuyacin hali kamar yadda wasu suke fata ba.

Shugaba Rauhani ya ci gaba da cewa, gwagwarmaya irin ta al’ummar kasar Lebanon wajen neman hakkokinsu da rayuwa  a cikin ‘yanci na siyas ada zamantakewa da tsaro, shi ne babban sirrin duk wata nasara da suka samu tun daga lokacin mulkin mallaka, har zuwa yanzu.

Haka nan kuma ya bayyana cewa kamar yadda kasar Iran ta kasane tare da Lebanon, za ta ci gaba da kasancewa tare da ita komai wahala komai dadi.

3936589

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ci gaba ، Shugaba Rauhani ، kasar iran ، kasar lebanon ، ‘yancin kai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: