IQNA

Jordan Ba Ta Amince Da Sauya Wuraren Tarihi Na Masalacin Quds Ba

23:00 - November 25, 2020
Lambar Labari: 3485399
Tehran (IQNA) Jordan ta ce ba za ta amince da duk wani sauyi wanda Isra’ila za ta gudanar a masallacin quds ba.

Gwamnatin kasar Jordan wadda ikon kula da masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus ke hannuta, ta bada sanarwan cewa ba za ta amince da duk wani sauyi wanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar a masallacin ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Daifullahi Ali-Alfa’iz ne ya bayyana haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa kofar babul Magaribah da kuma titin da ya shigo zuwa masallacin daga kofar zasu ci gaba da kasancewa kamar yadda suke, kamar yadda kuma hukumar UNECSO ta amince da hakan.

Daifullah ya kara da cewa tun shekara ta 1967 ne yahudawan sahyoniyya suka kwace iko da kofar Babul Magaribah, sannan a shekara ta 2000 ta maryarda aikin shigo da baki ‘yan yawon bude ido, wadanda ba musulmi ba zuwa cikin masallacin.

Gwamnatin kasar Jordan ce aka azawa nauyin kula da wuraren ziyara na musulmi da kiristoci a masallacin al-aqsa na birnin Qudus tun shekara ta alif da dari tara da arba’in da takwas.

 

3937305

 

captcha