Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, Hezbollah ta dai shigar da karar wani tsohon dan majalisar dokokin kasar da kuma wata jam’iyyar siyasar kasar kan yi mata wannan zargin.
A ranar hudu ga watan Agusta da ya gabata ne wata fashewa ta auku a tashar ruwa ta birnin Beirut, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da dari biyu da kuma jikatar wasu fiye da dubu shida da kuma haifar da babbar barna a birnin.
Bayan fashewar data auku jama’ar kasar da dama sun zargi mahukunta da manyan ‘yan siyasar kasar da yin sakaci wajen aukuwar lamarin.