IQNA

Dan Wasan Barcelona Ya Yanke Alaka Da Kamfanin Huawei Na China Domin Nuna Goyon Baya Ga Musulmi

23:06 - December 11, 2020
Lambar Labari: 3485448
Tehran (IQNA) Antoine Griezmann fitaccen dan wasan kwallon kafa na Barcelona ya yanke alakarsa da kamfanin waya na Huawei na China domin nuna goyon baya ga musulmin kasar.

Tashr DW ta abyar da rahoton cewa, dan wasan wanda dan kasar Faransa ne, ya sanar a shafinsa na Instagram cewa, samakon bayanan da ya samu kan ewa ana zargin kamfanin waya na Huawei da yin amfani da wata manhaja domin fayyace fuskokin musulmi na kabiral Igoir domin cutarsu, wannan yasa ya yanke shawarar kawo karshen alaka tsakaninsa da wannan kamfani.

Kamfanin bincike na IPVM da ke kasar Amurka ne ya bayar da wani rahoto bayan gudanar da bincike, inda ya ce ya gano cewa kamfanin Huawei ya saka wata manhaja da take fayyace fuskokin musulmin kasar, kuma manhajar tana aikewa da sako nan take ga jami’an ‘yan sanda.

Kungiyar kare hakkin bil adama da HRW ta bayar da bayanin cewa, daga shekara ta 2018, jami’an tsaron China sun kame musulmi ‘yan kabilar Igoir ta wannan hanya, sakamakon samunsu suna karatun kur’ani, ko saka tufafin kabilarsu ko na musulunci ko kuma yin tafiya zuwa kasashen waje, wanda gwamnatin China ta haramta musu yin hakan.

Antoine Griezmann wanda ya buga wa Faransa wasa gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha, ya kasance jakadan kamfanin waya na Huawei na China tun daga shekara ta 2017 ya zuwa yanzu.

3940329

 

 

captcha