IQNA

23:09 - December 11, 2020
Lambar Labari: 3485449
Tehran (IQNA) da dama daga cikin masana Amurkawa suna da imanin cewa, musulmin Amurka za su samu sauki wajen gudanar da harkokinsu na addini fiye da lokacin shugabancin Trump da ake nuna musu wariya.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da wani rahoto da ke cewa, musulmin Amurka suna da kyakkyawan zaton samun sauki wajen gudanar da harkokinsu na addini fiye da lokacin shugabancin Trump da suka fuskanci matsaloli masu yawa na wariya da tsangwama da aka yi ta nuna musu a hukumance.

Tun lokacin yakin neman zabe, Joe Biden ya halarci wani taron musulmi da aka gudanar ta yanar gizo, wanda kungiyar Emgage Action ta dauki nauyin shiryawa kan yadda musulmi za su kada kuri’a, wanda aka gudanar kai tsaye ta hanyar yanar gizo, wanda kuma Joe Biden yana daga cikin wadanda kungiyar musulmin ta gayyata.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Joe Biden ya bayyana cewa, kuri’ar musulmi miliyan daya tana da muhimmanci a wurinsa, a kan haka yana da bukatar kuri’u na dukkanin musulmi da suke cikin Amurka, kamar yadda kuma ya yi alkawalin cewa zai soke dokar da Trump ya kafa ta hana musulmi daga wasu kasashe shiga cikin Amurka.

Haka nan kuma Joe Biden ya bayyana Donald Trump da cewa yana a matsayin munkari ne, wanda manzon Allah Muhammad ya ce a kawar dad a hanu, ko da harshe ko kuma da zuciya, wanda shi ne mafi raunin imani, inda ya ce musulmi za su iya bayar da gudunmawa wajen kawar da Trump da kuri’unsu a lokacin zabe.

A wani rahoton da jaridar Jaridar Washington Post ta bayar a cikin baya-bayan nan, ta bayyana cewa, bisa ga bayanan da wasu makusantan Joe Biden suke yi, na tabbatar da cewa Biden na da nufin kawo karshen dokar nuna wariya ga wasu daga cikin kasashen musulmi da Donald Trump ya kafa, wanda hakan ke nufin zai baiwa musulmi damar yin walwala  cikin ‘yanci a cikin kasar Amurka.

Tun a cikin shekara ta dubu biyu da sha bakwai, Trump ya kafa dokar da ta haramta wa wasu kasashen musulmi izinin shiga cikin kasar Amurka, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen kasar ta Amurka.

A nata bangaren babbar kungiyar musulmin kasar ta Amurka ta fitar da wani bayani da ke cewa, kungiyar tana kiran Joe Biden da mayar da hankali wajen aiwatar da alkawullan da ya dauka, musamman na kare hakkokin musulmia kasar Amurka, tare kawo karshen nuna musu wariya a kasar.

A cikin shekaru hudu da Donald Trump ya yi yana mulkin Amurka, musulmi sun fuskanci matsaloli masu tarin yawa akasar, domin kuwa a lokacin mulkinsa ne kyamar musulmi ta kara tsananta a kasar Amurka, sakamakon irin kalaman da yake na tozarta musulmi da kuma yin batunci a kansu.

Da dama daga cikin musulmin kasar ta Amurka suna da imanin cewa, gwamnatin Biden za ta yi kama da gwamnatin Obama ta fuskoki da dama, daga ciki har da baiwa musulmi damar gudanar da harkokinsu na addini cikin ‘yanci a cikin kasar Amurka.

 

3939611

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: