IQNA

Wasu Da Ba A San Ko Su Wane Ne Ba Sun Kashe Limamin Wani Masallai A Jamus

23:49 - December 25, 2020
Lambar Labari: 3485492
Tehran (IQNA) wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kashe limamin masallaci a garin Stuttgart na kasar Jamus.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatar shari’a ta kasar Jamus ta bayar da sanarwar cewa, a jiya wasu mutane wadanda ba a san ko su wane ne ba, sun kashe limamin wani masallaci a garin Stuttgart na kasar Jamus.

Bayanin ya ce mutumin dan asalin kasar Pakistan ne wanda yake limanci a wani masallaci da ke ikin birnin na Stuttgart.

Lamarin ya faru ne a lokacin da suke yin tattaki tare da matarsa a cikin wani wurin hutawa da mutane suke zama, inda kwatsam sai wasu mutane biyu dauke da wukake suka kai musu hari.

Sakamakon yadda suka yi ta daba masa wuka ya samu munan raunuka da kuma zubar da jinni mai yawa, wanda sakamakon haka a nan take rasu.

Mutanen da suka aikata wannan laifi dai sun tsere, amma jami’an tsaron kasar ta Jamus sun ce sun shiga gudanar da bincike kan lamarin, domin gano wadanda suka aikata wannan laifi domin su fuskanci hukunci.

3943114

 

 

 

captcha