IQNA

Shekara ta 2020 Abubuwa Daban-Daban Sun Faru A Gabas ta Tsakiya

22:57 - December 26, 2020
Lambar Labari: 3485493
Tehran (IQNA) Shekara ta 2020 ta kasance cike da abubuwa da suka faru a duniya wadanda suka dauki hankulan dukkanin al’ummomin duniya musamman annobar korona wadda ta girgiza duniya.

Yankin yammacin Asia na daga yankunan duniya da suka fuskanci abubuwa da dama da suka faru daga karshen shekara ta 2019 zuwa cikin shekara ta 2020 mai karewa.

Daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankula a farkon shekara ta 2020 shi ne batun kisan gillar da Amurka ta yi wa babban kwamandan sojin kasar Iran Janar Qassem Sulaimani, lamarin da ya kusa jefa yankin baki daya a cikin tashin hankali.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Karin matsin lamba a kan masu neman canji daga tsarin mulkin mulukiya a kasashen Saudiyya da Bahrain, da kuma yadda aka rika yi musu yankan rago da fille kawunansu, saboda sun nemi a yi gyara a cikin tsarin yadda ake tafiyar da mulki da ddukiyar al’ummar kasa ta kaita ga wasu ‘yan tsirarun mutane ‘yan gida guda wadanda suma ‘yan kasa ne kamar kowa.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Hankoron wasu daga cikin kasashen larabawa wajen neman kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, ta yadda suka amince su yi watsi da kauda kai daga irin mawuyacin halin da gwamnatin yahudawan ta jefa ‘yan uwansu larabawan Falastinu a ciki.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Matsalolin cikin gida da Isra’ila take fama da su na siyasa da tattalin arziki, wanda kuma hakan ne yasa yahudawa suke zanga-zangar neman Netanyahu ya sauka daga kan mulki, yayin da kuma wasu gwamnatocin larabawa suke kokarin ganin sun taimaka masa domin magance matsalolin tattalin arzikin da gwamnatinsa take fuskanta, domin shawo kan boren da yahudawa suke yi masa.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Tsanantar mawuyacin halin da al’ummar Yemen suke ciki, sakamakon yakin da gwamnatin Saudiyya ta kaddamar a kan al’ummar kasar tun kimanin kusan shekaru shida da suka gabata da sunan yaki da ‘yan kungiyar alhuthi wadanda ba ta dasawa da su, inda ya zuwa yanzu Saudiyya ta kashe dubban fararen hula mata da kanan yara da tsoffi kamar yadda rahotannin majalisar dinkin duniya suka tabbatar.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Fashewar wasu abubuwa da ta faru a tashar jiragen ruwa ta Beirut a kasar Lebanon, wanda ya yi sanadiyyar mutate mutane fiye da 200 da jikkatar wasu dubbai, wanda ya faru sakamakon ajiye wani jirgin ruwa da yake dauke da kayayyaki masu fashewa, wanda ya kwashe shekarua  wurin.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Sake mayar da tsohon wurin tarihin nan na birnin Istanbul zuwa masallaci wato hagia Sophia, wanda dama ya taba kasancewa masallaci daruruwan shekaru da suka gabata, wanda kuma a halin yanzu an mayar da shi ana ci gaba da yin salla a cikinsa.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Yakin da ya auku ayankin Karabakh tsakanin Armenia da kuma Azerbaijan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban sojoji daga bangarorin biyu gami da kuma fararen hula.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Karuwar halin zaman dar-dar a yankunan Jamu da Kashemir, sakamkaon irin matakan da gwamnatin kasar India take dauka a halin yanzua  kan musulmi an wadannan yakuna, musamman a cikin wannans hekara ta 2020 mai karewa.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

Sulhu tsakanin bangarorin siyasar kasar Afghanistan, musamman tsakanin gwamnati da kuma mayaka masu tayar da kayar baya, wanda har yanzu ya kasa tabbata.

تاثیر خاورمیانه‌ای بر سیاست بین‌الملل

3942727

 

 

 

captcha