Shararren makarancin kur’ani dan kasar Iraki Rafe Al-amiri ya gabatar da karatun kur’ani mai tsarki aya ta 73 a cikin surat Zumar ga ruhin Sulaimani da Muhandis a wurin taron tunawa da cikar shekara guda da shahadarsu.
Matanin Ayar:
Kuma aka tura waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a- jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, « Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama ( a cikinta ).