IQNA

Tilawar Muhammad Badr Hussain A Babban Masallacin Tarihi Na Alkahira

20:33 - January 04, 2021
Lambar Labari: 3485523
Tehran (IQNA) tilawar kur’ani mai tsarki daga bakin marigayi Muhammad Badr Hussain a babban masallacin birnin Alkahira na Masar.

An haifi wannan babban makarancin kur’ani mai tsarki a cikin shekara ta 1937 a garin Santa da ke cikin gundumar Tanta a yammacin kasar Masar, wanda ya hardace kur’ani mai tsarki tun yana karami.

Tun a cikin shekara ta 1968 ya kammala karatun jami’a a jami’ar Azhar a bangaren usul, daga nan kuma ya mayar da hankali ga lamarin kur’ani.

Ya rasu a ranar 28 ga watan Maris, kuma za a iya sauraren wannan kira’a tasa da ya yi a masallain tarihi na Muhammad Ali:

 

3945526

 

 

 

 

 

captcha