Kotun birnin Bagadaza na kasar Iraki ta bayar da sammacin kamo shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump, bisa laifin kisan mataimakin babban kwamandan dakarun sa kai na al’ummar Iraki, Abu Mahdi Almuhandis.
A yau Alhamis kotun Rasafah da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki, ta fitar da bayani da ke dauke da bayar da sammacin kamo shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump, wanda ya bayar da umarnin kisan mataimakin babban kwamandan dakarun Hashd Al-shaabi, Abu Mahdi Almuhandis tare da wadanda yake tare da shi da suka hada da Kasim Sulaimani.
Bayanin babban alkalin kotu kuma mai bincike, ya bayyana cewa, sakamakon karar da aka shigar a gaban kotun kan kisan Abu Mahdi Almuhandis, da kuma binciken da kotun ta gudanar kan hakan, ta tabbatar da cewa Donald Trump yana da hannu a cikin kisan.
A kan haka ya ce kotun Rasafah ta bayar da sammacin kamo Donald Trump domin gurfanar da shi a kan laifin kisa.
Alkalin ya kara da cewa, akwai sauran mutane da ake bincike kansu, kuma za afitar da sunayensu domin bayar da sammaci a kan duk wanda laifinsa ya tabbata a cikin kisan, ko Amurkawa ne ko Irakawa.