IQNA

Kwamitin Musulmin Habasha Ya Bukaci A Hukunta Wadanda Suka Rusa Masallacin Tarihi Na Najashi

22:02 - January 08, 2021
Lambar Labari: 3485536
Tehran (IQNA) kwamitin musulmin kasar Habasha ya bukaci da a hukunta wadanda suke da hannu wajen rusa masallacin tarihi na Najashi.

Shafin yada labarai an al’ain ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Qasem Muhammad Tajuddin babban sakataren kwamitin musulmin kasar Habasha ya bukaci da a kama wadanda suke da hannu wajen rusa masallacin tarihi na Najashi, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya ce muna kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin tabbatar da cewa an kamo duk wadanda suke da hannu wajen rusa ginin tsohon masallacin tarihin kasar, domin kuwa a cewarsa wannan wurin tarihi ne na muslunci da kuma kasar Habasha.

Tajuddin ya ce yanzu sun mika wannan bukata a hukumance ga gwamnatin Habasha, kuma ana bin kadun lamarin.

Masallacin tarihi na Najashi dai yana a yankin Tigray ne, yankin da ke fama da matsaloli na ‘yan arewa, wanda ked a tazarar kimanin kilo mita 900 a arewacin birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar.

Gwamnatin Habasha dai ta dora alhakin rusa wannan masallaci da aka gina tun fiye da shekaru 1400 da suka gabata, a kan ‘yan arewan yankin da suke dauke da makamai

3946344

 

 

captcha