IQNA

Tarayyar Turai Ta Yi Watsi Da Saka Kungiyar Ansarullah (Alhuthi) Cikin ‘Yan Ta’adda Da Amurka Ta Yi

21:58 - January 13, 2021
Lambar Labari: 3485551
Kungiyar tarayyar turai ta yi watsi da matakin Amurka na saka kungiyar Ansarullah ta Yemen a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shafin yada labarai na kungiyar tarayyar turai ya bayar da bayanin cewa, kakakin babban jami’i mai kula da siyasar wajen kungiyar Peter Stano ya bayyana cewa, daukar wannan mataki na saka kungiyar Ansarullah cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda ba abu ne da kungiyar tarayyar turai za ta amince da shi ba.

Ya ce Amurka ta sani sarai kan cewa, daukar wannan mataki babu abin da zai kara haifarwa a kasar Yemen sai kara dagula lamurra, maimakon daukar matakin da zai taimaka wajen warware matsalolin siyasar kasar ta hanyar sulhu da fahimtar juna tsakanin dukkanin al’ummomin kasar.

Daga karshe ya ce kungiyar tarayyar turai tana maraba da duk wani mataki da zai kara kusanto da al’ummomin kasar Yemen wuri guda, maimakon tarwatsa su da kara rarraba kawunansu a cikin wannan mawuyacin hali da kasar take ciki.

A daidai lokacin da kungiyar tarayyar turai take yin Allawadai da wanann mataki na Amurka kan saka kungiyar ansarullah cikin kungiyoyin 'yan ta'adda, gwamnatocin kasashen Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa sun fito sun yaba wa Amurka kan hakan.

 

3947387

 

 

captcha