IQNA

Zaman Makokin Shahadar Fatima Zahra (AS) Tare Da Halartar Jagoran Juyi Na Iran

17:46 - January 17, 2021
Lambar Labari: 3485561
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman makokin shahadar Fatima Zahra (AS) tare da halartar jagoran juyin juya halin musulunci a Husainiyar Imam Khomeini (RA)

A yau ne ake gudanar da tarukan tunawa da zagayoar lokain shahadar Sayyida Fatima Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta diyar manzon (SAW) fiyayyen dukkanin talikai.

A daren jiya an gudanar da taron makokin tare da jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khameni, amma an takaita halartar jama'a a wurin saboda yanayin da ake ciki, da kuma matakai na kiwon lafiya.

An bayani kan matsayin iyalan gidan manzon Allah da kuma abin da suka gadar wa al'ummar musulmi na shiriya bisa tafarkin manzo (SAW) wanda kuma Sayyida Zahra ita ce wadda tsatson manzon Allah ya wanzu ta hanyarta, saboda ita kadai ce ta haifi jikoki ga manzon Allah wadanda tsatsonsu mai albarka ya wanzu har kasa ta nade.

 

3948162

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :