IQNA

Faransa: Firayi Minista Ya Yi Watsi Da Daftarin Dokar Hana Kanan Yara Mata Saka Hijabi

22:43 - January 19, 2021
Lambar Labari: 3485567
Tehran (IQNA) Firayi ministan kasar Faransa ya nuna rashin amincewarsa da daftarin dokar da aka gabatar a majalisa, na neman a hana kananan yara mata saka hijabi a makarantun kasar.

Tashar Blooberg ta bayar da rahoton cewa, Jean Costex firayi ministan kasar Faransa, ya bayyana rashin amincewarsa da daftrain dokar da aka gabatar, na hana yara mata musulmi saka hijabi a makarantu a fadin kasar Faransa.

Ya ce wannan ya saba wa ka’ida, kuma yana a matsayin danne hakkokin wasu ne na bin koyarwar addinin da suka yi imani da shi, a kan haka ya ce, shi ba taba amincewa da hakan ba.

Wata ‘yar majalisar dokokin kasar Faransa daga jam’iyyar shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ce ta gabatar da wannan shawara a gaban majalisar dokokin kasar ta Faransa, inda kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar suka goyi bayan haka, amma dai ba a riga an kada kuri’a domin amincewa da hakan a matsayin doka ba.

Wasu masana da ke bin diddigin siyasar kasar Faransa sun yi imanin cewa, Emmanuel Macron da ke son sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa, ya dauki salon siyasar nuna kiyayya ga musulmi ne da nufin burge masu tsatsauran ra’ayin kin jinin musulmi a  kasar, domin samun kuri’unsu a zabe mai zuwa.

A cikin shekara ta 2004 Faransa ta haramta nuna duk wasu alamu na addini a cikin makarantu, a shekara ta 2010 kuma ta haramta saka nikabi a cikin makarantun kasar baki daya.

3948589

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :