IQNA

Iran Ta Mayar Da Martani Mai Zafi A Kan Burtaniya, Jamus, Faransa, Dangane Da Shirinta Na Nukiliya

22:53 - January 19, 2021
Lambar Labari: 3485569
Tehran (IQNA) Ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani mai zafi a kan kasashen Burtaniya, Jamus, Faransa, dangane da shirinta na nukiliya.

Kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, kasashen turai uku da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tare da Iran, wato Burtaniya, Jamus, Faransa, ba su da hurumin yin wani korafi dangane da shirin nukiliya na Iran, domin kuwa ba su yi aiki da alkawullan da suka dauka ba.

Ya ce dangane da batun yin amfani da karfen uranium a cibiyar nukiliya da ke Isfahan, yin hakan bai saba wa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta duniya ba

Khatib Zadeh ya ce ana yin amfani da wannan karfen uranium a bangaren ayyuka na farar hula, domin kuwa akwai bangarorin na kiwon lafiya da ake yin amfani da shi, wanda kuma kowace kasa ta duniya tana da hakkin yin hakan.

Ya ci gaba da cewa, yin amfani da wannan batu domin cimma manufofi na siyasa ba abu ne da ya dace ba, abin da yake da muhimmanci shi ne kowane bangare ya yi aiki da abin da yake bisa doka.

Iran tana kokawa dangane da yadda kasashen turai suka kasa cika alkawullan da suka dauka dangane da yarjejeniyar nukiliya, wanda hakan ne yasa ta jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniya, inda a baya-bayan nan ta fara tace sanadarin uranium kashi ashirin cikin dari, wanda kasashen turan ke cewa Iran za ta iya kera makaman nukliya da shi.

3948601

 

captcha