IQNA

Makaranta Kur’ani 120 Ne Suke Halartar Gasar Kur’ani Ta Duniya Ta Hanyar Yanar Gizo

23:38 - January 20, 2021
Lambar Labari: 3485571
Tehran (IQNA) makaranta kur’ani mai tsarki 120 ne suke halartar gasar kur’ani ta duniya a Iran ta hanyar yanar gizo.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, ya zuwa yanzu an shiga mataki na kusa da na karshe a gasar kur’ani ta duniya a Iran da ke gudanarwa ta hanyar yanar gizo.

Gasar dai ana gudanar da ita ne karo na talatin da bakawai, kuma makaranta da mahardata 120 ne suke halartar gasar kai tsaye ta hanyar yanar gizo daga kasashe 20 na duniya.

Muhimman bangarorin gasar dai sun hada da kira’a, inda ake la’akari da hukunce-hukunce na karatu, bayan nan kuma akwai tafsiri da kuma harda a dukkanin matakai.

A kowace shekara dai ana gudanar da wannan gasa ne tare da halartar makaranta daga sassa na duniya, amma a shekarar bana sakamakon matsaloli da suka shafi kiwon lafiya, ana gudanar da gasar ne kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Daga karshe za a fitar da wadanda suka fi nuna kwazo domin ba su kyautuka na musamman, bayan kyautuka na bai daya da za a bayar ga dukkanin wadanda suka shiga gasar.

3948639

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :