Shugaban Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau, dangane da zagayowar lokacin gudanar da bukukuwan samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, wanda ya cika shekaru 42 a yau.
Rauhani ya ce tun bayan samun nasarar juyin juya hali Iran take fuskantar matsin lamba da takunkumi daga gwamnatin Amurka, amma a cikin shekaru uku da suka gabata, kasar ta fuskanci takunkumai mafi tsanani a karkashin gwamnatin Trump da nufin durkusar da kasar baki daya.
Shugaba Rauhani ya ce, a cikin wadannan shekarun ne kuma kasar ta samu wasu manyan nasarori da bat a samu a baya ba, a bangaren bunkasa sana’ointa na cikin gida, da kuma dogaro da kanta.
Bayan haka ya kara da cewa, a cikin wadannan shekaru uku kasar ta samar da abubuwa na kasuwanci da take fitarwa zuwa kasashen ketare wadanda ba su da dangantaka da arzikin danyen man fetur da dangoginsa, wanda a shekara tana samun fiye da dala biliyan 30 ta hanyarsu.
Haka lamarin yake a bangaren samar da kayayyakin kiwon lafiya, noma, madatsun ruwa, karfin wutar lantarki, da kuma bangaren ayyuka na nukiliya, da kuma samar da muhimman kayayyaki na soji da sauran ayyukan tsaro.
Wanda kuma a cewarsa dukkanin wadannan abubuwa an samu gagarumin ci gaba wajen samar da su ne a cikin wadannan shekaru da aka tsananta takunkumin zalunci a kan kasar ta Iran.